Harin dai ya auku ne a daidai lokacin al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki a yau Laraba.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko Da'esh ta fitar da wata sanarwa a ashafin yada farfaganta na Amaq cewa ita ce ke da alhakin kai harin.
Bayanai sun ce an kai harin ne jim kadan bayan wani harin gurneti a wani ofishin zabe a lardunan Khuzdar da Baloutchistan, inda wani jami'in yan sanda guda ya mutu, wasu uku kuma suka raunana